Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - bayyana cewa kamfanin jiragen sama na Air France da na gwamnatin Senegal da na kasar Ivory Coast duk sun tsaida tafiye tafiyensu zuwa kasar ta Mali a jiya Litinin har sai abinda hali yayi.
Banda haka kasashen sun bada labarin rufe dukkan kan iyakokin kasashensu da da kasa ta Mali don tabbatar cewa da takunkuman tattalin arzikin suna aiki.
Sai dai shugaban kasar ta Mali Assimi Goita ya bayyana cewa kasarsa tana da wasu hanyoyi wadanda zata bi don maida takunkuman tattalin arzikin da ECOWAS ta dora mata marasa tasiri.
A ranar lahadin da ta gabata ce shuwagabannin kungiyar ta ECOWAS, a wani taro na musamman da suka gudanar a birnin Accra na kasar Ghana suka bukaci kasar Mali ta gudanar da zabubbuka a cikin watan Fabrairu mai zuwa kamar yadda tayi alkawari tun farko ko kuma wadannan takunkuman su ci gaba da aiki har zuwa lokacinda ta gudanar da zabubbuka a kasar.
342/